Ciwon Sukari Nau'i na Biyu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ciwon Sukari Nau'i na Biyu



Hoto: WHO International


Gabatarwa

Hukumar Lafiya ta duniya, wato WHO (2020), ta siffata ciwon sukari nau’i na biyu, type 2 diabetes, da cewa shi ne ciwon sukarin da ya fi shahara wanda yake faruwa daga gazawar aikin ƙwayar halitta da ake kira beta sel , wato beta cell (β-cell) kenan a Turance wajen samar da sinadarin insulin da kuma bijirewa sinadarin insulin da jiki ke yi, wadda kuma abar dangantawa ce da nauyi da kuma ƙiba masaras misali.

Ra’ayin Cerf (2013), ya ƙarfafi wannan magana ta WHO, inda ya bayyana cewa: “Duka biyu; gazawar aikin beta sel da bijirewar sinadarin insulin da jiki ke yi suna haifar da hauhawar sinadarin bilkodi a cikin jini wadda kuma hakan alama ce ta samuwar cutar sukari nau’i na biyu”.

Ita kuwa NIDDK (2016); wato National Institute of Diabetes and Digestive and Kidney Disease ta Amurka, siffata ciwon sukari nau’i na biyu ta yi da cewa: “Idan kana ɗauke da ciwon sukari nau’i na biyu, to jikinka baya samarwa ko aiki da sinadarin insulin yadda ya dace”.

Kenan, da zarar jiki ya ƙaranta samar da sinadarin insulin, wadda hakan ke afkuwa daga ƙarancin aikin beta sel kamar yadda muka gani, ko kuma jikin baya sarrafa sinadarin insulin yadda ya dace sakamakon bijerwar da sinadarin insulin ɗin yake yi wa jiki, to cutar sukari nau’i na biyu ta tabbata. Wannan kuma shi ne abin da ya bambanta ta da ciwon sukari nau’in farko, wadda shi ƙwayoyin halittar da abin ya shafa kasa samar da sinadarin insulin ɗin suke yi.

Barazana

Abin da ake nufi da barazana a nan, shi ne mutanen da ke fuskantar barazanar kamuwa da wannan cuta duk da cewa kowa ma yana iya kamuwa da ita ciki kuma har da ƙananan yara kamar yadda bincike ya tabbatar. Amma duk da haka, NIDDK (2016), sun zayyana waɗannan mutane a matsayin waɗanda suka fi kowa fuskantar barazanar kamuwa da wannan cuta. Rukunin mutanen su ne:

  • Mutumin da ya haura 45.
  • Zuriyar da ke da tarihin cutar sukari.
  • Mutane masu nauyi maras misali.
  • Mutanen marasa motsa jikinsu.
  • Ƙabila da ma’ana ta race.
  • Mutane masu hawan jini.
  • Mutane masu ɗauke da gajeren ciwon sukari da kuma ciwon sukari yayin goyon ciki.

Alama

Kirkpatrick (2021); Healthline (2018) sun haɗu a kan waɗannan alamomi cewa samuwar wasu daga cikinsu na alamta samuwar ciwon sukari nau’i na biyu:

  • Jin matsananciyar yunwa.
  • Jin matsananciyar ƙishirwa.
  • Yawan yin fitsari.
  • Rashin nauyi maras misaltuwa.
  • Gajiya ba tare da aiki ba.
  • Matsalolin fatar jiki.
  • Rashin warkewar rauni da wuri (ƙanjiki).
  • Kumburin ƙafa ko yatsun ƙafa.
  • Gani dishi-dishi.
  • Kumburin da baya warkewa da wuri. Da sauransu.

Illoli

Illolin wannan cuta suna da yawa, amma dai waɗanda suka fi yawan afaruwa su ne cewa tana haifar da:

  • Cututtukan zuciya (heart diseases).
  • Shanyewar tsagi ko ɓarin jiki (stroke).
  • Cutar hanta (kidney disease).
  • Matsalolin ido (eye problems).
  • Ciwon haƙora/dasashi (dental disease).
  • Lalacewar jijiya (nerve damage).
  • Larurorin ƙafa (foot problems) da sauransu.

Kariya

NIDDK (2016), ta bayyana cewa, “Cin kyakkyawan abinci, aikin ƙarfi da kuma nisantar shan taba sugari zai hana kamuwa ko kuma ya jinkirta kamuwa da ciwon sukari nau’i  na biyu”.

Magani

Ana iya warkewa tsaf, daga ciwon sukari nau’i na biyu ta hanyar:

  1. Ingantaccen Abinci: Samun ingantaccen abinci mai gina jiki, wadda ke da wadatattun sinadaran maiƙo da furotin, zai bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen yaƙar wannan cuta.
  2. Motsa Jiki: Yawan motsa jiki ko da ta hanyar tafiya ne, yana bayar da gagarumar gudunmwa wajen fatattakar ciwon sukari nau’i na biyu.
  3. Yawan amfani da waɗannan na’ukan cimaka guda ashirin da za a lissafo a ƙasa:
    • Girf ko Kirfa.

    • Hoto: Hub Pages

    • Habbatussauda.
    • Jinsin (Ginseng).

    • Hoto: Life Hack

    • Albasa.
    • Koren Shayi (Green tea).
    • Citta.
    • Tafarnuwa.
    • Alobera.
    • Kabeji.
    • Wake.
    • Kokumba.
    • Kifi.
    • Man Zaitun.
    • Alayyaho.
    • Dankalin Hausa.
    • Kuɓewa.
    • Shuwaka.
    • Nanar Shayi.
    • Ganyen Kabewa.
    • Kankana Mai Ɗaci (Bitter Melon).

    • Hoto: Organic Authority

Allah ka bai wa dukkan masu ɗauke da wannan cuta lafiya.

Manazarta:


Cerf M.E. (2013). Beta Cell Dysfunction and Insulin Resistance. An ciro a 2021, daga https://www.ncbi.nlm.nih.gov/pmc/articles/PMC3608918/

Healthline (2018). Everything You Need to Know About Diabetes. An ciro a 2021, daga https://www.healthline.com/health/diabetes

Healthy Direction (2021). 12 Herbs for Diabetes. An ciro a 2021, daga https://www.healthydirections.com/articles/blood-sugar/herbs-for-diabetes

Jovanov D. (2017). Herbs and Spices for Diabetes. International Journal of Nutritional Science & Food Technology. 3:1, 26-29. DOI: 10.25141/2471-7371-2017-1.0026

Kirkpatrick N. (2021). What Are Signs & Symptoms Of Childhood Diabetes? An ciro a 2021, daga https://www.betterhelp.com/advice/childhood/what-are-signs-symptoms-of-childhood-diabetes/

NIDDK (2016). What is Diabetes? An ciro a 2021, daga https://www.niddk.nih.gov/health-information/diabetes/overview/what-is-diabetes

WHO (2020). Hearts-D Diagnosis and Management of Type 2 Diabetes, An ciro a 2020, daga WHO-UCN-NCD-20.1-eng.pdf


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub